Nkurunziza ya samu damar ci gaba da mulki
May 21, 2018Shugaba Pierre Nkurunziza na kasar Burundi ya samu nasarar ci gaba da mulkin kasar har zuwa shekara ta 2034 sakamakon nasarar samun kuri'un amincewa yayin gyaran kundin tsarin mulkin kasar, kamar yadda hukumar zaben kasar ta sanar.
Kashi 73.26 cikin 1000 na al'ummar kasar ne suka zabi amincewa da zarcewar mulkin shugaban kasar mai shekaru 54 yayin zaben raba gardama da aka gudanar a ranar Alhamis data gabata,
Har ya zuwa yanzu dai dokokin tsarin mulkin kasashen gabashin Afrika sun amince da mulkin zango biyu na shekaru biyar-biyar ga shugabanninsu, lamarin da a halin yanzu ya samu kwaskwarimar da ta mayar da shi shekaru bakwai-bakwai.
Tun da fari masu adawa da wannan karin wa'adi na shugaban kasar ta Burundi sun yi ta kiraye-kiraye ga al'ummar kasar da su kaurace wa wannan zabe