SiyasaJamus
Nukiliya: Iran ta ce babu ruwanta da Amirka
October 28, 2021Talla
Ministan harkokin wajen Iran, Ali Bagheri, ya ce kasarsa ba za ta yi wani zama da Amirka ba, kasashen kawai da za ta gana da su game da nukiliyar su ne; China da Faransa da Birtaniya da Rasha da kuma Jamus.
Taron wanda zai dora a kan yarjejeniyar 2015 da za a yi shi cikin watan gobe na Nuwamba, na da munufar hana Iran din damar iya kera makaman bom da makamashin nukiliyar.
A cewar kasashen yin hakan ne zai bai wa Iran damar fita daga jerin takukuman da aka kakaba mata.
Wannan batu dai ya fada sarkakiya ne, bayan janye Amirka daga yarjejeniyar da tsohon shugabanta Donald Trump ya yi a shekarar 2018.