Pyongyang za ta aminta da masu bincike
October 8, 2018Talla
Pompeo ya yi wadannan kalamai ne bayan ganarwasa da jagoran na Koriya ta Arewa Kim Jong Un a birnin Pyongyang, inda ya ce an samu ci gaba sosai kan batun nukiliyar kasar ta Koriya ta Arewa. A watan mayu ne dai da ya gabata, Koriya ta Arewa ta wargaje wurin da take yin gwaje-gwajenta na manyan makamai masu cin dogon zongo da ma na nukiliya, sai dai kuma har ya zuwa yanzu Koriya ta Arewan ba ta ba da izinin shiga yankin ga masu bincike ba. Daga bisani sakataran harkokin wajen na Amirka ya bar Koriya ta Arewa zuwa birnin Pekin na kasar Chaina, inda zai kammala ziyarar da ya soma a yankin Asiya, wadda da farko ta kai shi a Koriya ta Kudu da kuma Japan.