1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nuri Al Maliki ya ziyarci Turquia

August 7, 2007

Irak da Turkiyya sun rattaba hannu a kan wata yarjeniya, ta haɗa ƙarfi domin yaƙar yan tawayen Ƙurdawa na PKK.

An cimma wannan yarjejeniya a sakamakon ziyara aikin da Praminista Nuri Al Maliki ya kai a birnin Ankara yau talata.

Ƙasashen 2 na zargin yan tawayen Ƙudawa na PKK, ta tada masu hargitsi, a game da haka ya zama wajibi inji sanarwar, su gama ƙarfi da ƙarfe, domin maido kwanciyar hankali a arewancin ƙasar Irak, yankin da yan tawayen ke anfani da shi, domin kai hare-haren.

Nur Al Maliki ya gudanar da wannan ziyara, a daidai lokacin da rikicin siyasa ke ƙara tsamari a birnin Bagadaza, inda wasu ƙarin ministoci 4 su ka yi murabus daga gwamnati.

Dag jimilar ministoci 40 da wannan gwamnati ta ƙunsa, a halin yanzu 17 su ka yi murabus daga muƙamin su.

A wani labarin kuma, ƙasar Danmark ta yanke shawara janye dakarun ta daga Irak.