Obama ya ce koriya ta Arewa ta kiyaye shi
April 5, 2013Kakakin shugaba Barack Obama na Amirka ya ce gwamnatinsu na cikin shirin ko ta kwana domin sa kafar wando guda da Koriya ta Arewa idan ta kuskura kai musu hari. Kakakin ya kuma kira barazanar shiga yaki da koriya ta Arewa ke yi tamkar abin da aka saba ji aka kuma saba gani.
Tun da farko shugaban sojin Koriya ta Arewa ya ce kasar ta yi shirin kai hare-haren makaman kare dangi akan Amirka. Sai dai gwamnatin Amirka ta yi kira ga ta koriya ta Arewa da ta daina nuna take-taken shiga yaki. A dai halin da ake ciki yanzu Koriya ta Kudu ta ce za ta janye dukannin ma'aikatanta da ke yankin Kaesong da take aikin hadin gwiwa ttare da Koriya ta Arewa in har ci gaba da zamansu a can zai iya zama wata barzana a gare su.
Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe