Obama ya gana da shugabannin Jamus da Faransa da Italiya
May 31, 2012Tattaunawar dai wadda aka yi ta kafar sadarwar Videoconference ta biyo bayan wadda shugabannin su ka yi yayin taron ƙasashen nan takwas masu ƙarfin arziƙin masana'antu na G8 wanda aka yi a Amurka a tsakiyar wannan watan da mu ke ciki.
Kazalika shugabannin sun zanta dangane da halin da ake ciki a ƙasar Siriya da ma dai tunanin da su ke da shi na kawo ƙarshen tashin-tashina da zub da jinin da ya ke cigaba da aukuwa tsakanin dakarun gwamnatin ƙasar ta Siriya da kuma masu rajin kawo sauyi.
Shugabannin har wa yau sun jaddada buƙatar da ke akwai na samun sauyi a ƙasar ta Siriya da nufin fidda ita daga halin da ta tsinci kanta a ciki domin kare rayukan fararen hula daga salwanta da kuma jikkata da su ke yi a kulli yaumin.
Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Mohammad Nasiru Awal