Obama ya gana da shugabannin yankin Gulf
April 21, 2016Talla
A wannan Alhamis Shugaban Amirka Barack Obama ya gana da manyan jami'an kasashen Larabawa shida inda suka tattauna kan batutuwan tsaro a yankin tekun Pasha da kuma yaki da kungiyar IS mai da'awar kafa Daular Musulunci a Iraki da Siriya. Obama ya gana da shugabannin kasashen Saudiyya da Kuwaiti da Qatar da Bahrain da Oman da kuma Hadaddiyar Daular Larabawa a birnin Riyadh. A taron inda kuma aka tabo maganar samar da kwanciyar hankali a yankin da rage zaman dar-dar tsakanin kasashen Larabawa da Iran, ya zo ne bayan makamancinsa da aka gudanar bara a Camp David da ke a Maryland. Kasashen Larabawa na nuna rashin jin dadinsu da irin kusancin da ake samu yanzu tsakanin Amirka da Iran.