1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Obama ya sauka a kasar Jamus

Salissou Boukari
November 16, 2016

Da yammacin wannan Laraba 16.11.2016 ne shugaban kasar Amirka mai barin gado Barack Obama ya sauka a filin jirgin sama na Berlin babban birnin kasar Jamus, a wata ziyarar bankwana da ya fara a wasu kasashen Turai.

Deutschland USA Besuch Präsident Barack Obama in Berlin, Abschied
Hoto: Reuters/F. Bensch

Wannan ziyara ta Barack Obama dai da ke matsayin ta bankwana a matsayinsa na shugaban kasar Amirka, ya faro ta ne daga kasar Girka inda a nan Jamus zai gana da shugabar gwmnati Angela Merkel, kafin wata tattaunawa da zai halarta tare da Merkel din da kuma Firaministan Italiya data Britaniya da kuma shugabannin kasashen Faransa da Spain a ranar Alhamis.

Hakan na zuwa ne a dai-dai lokacin da kasashen na Tarayyar Turai ke nuna shakkunsu dangane da sabuwar tafiyar da za su yi da Amirka, tun bayan zaben Donald Trump a matsayin sabon shugaban kasa wanda a baya ya soki lamirin tsarin kungiyar tsaro ta NATO da kuma neman canza wasu yarjejeniyoyi da aka cimma a tsakanin Amirkan da nahiyar ta Turai. Sai dai ana ganin shugaban mai barin gado Barack Obama na kokarin kwantar da zukatan shugabannin na Turai.