Obama ya taya Buhari murnar lashe zabe
April 1, 2015![Mohammadu Buhari](https://static.dw.com/image/18350777_800.webp)
Hakan na kunshe cikin sakon Obama zuwa ga al'ummar Najeriya, da acewarsa ko shakka babu na tabbatar da matsayin kasar na uwa mabada mama a nahiyar Afirka. Kan haka ne ya yi kira ga magoya bangarorin biyu da su ci-gaba da martaba demokradiyya ta hanyar darajawa sakamakon zaben, domin ci-gaban zamantakewa tsakanin al'umma da hadin kan kasa.
Shi ma a nashi sakon taya murna ga Buhari, babban sakataren MDD Ban Ki-moon, yabawa 'yan Najeriyar ya yi da cewar, sun taka rawar azo a gani. Ya ce gudanar da zaben cikin nasara na tabbatar da cewar yanzu Najeriya ta zama ja gaba a fannin demokradiyya. Ki-moon ya yi fatan cewar irin wannan halin sanin ya kamata ne zai kasance a zaben gwamnoni da na 'yan majalisar jiha da ke tafe a ranar 11 ga watan Afrilu. Acewarsa dai wannan yanayi abun yabawa ne, domin shi ne karon farko da wata gwamnatin farar hula za ta mika mulki zuwa ga wata, a wannan kasa da tafi ko wacce yawan jama'a a nahiyar Afrika.
Sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya shawarci 'yan takarar da ke da wani korafi da su gabatar da shi a hukumance.