Obama ya yabawa Faransa kan yakin Mali
January 26, 2013Talla
Obama ya furta hakan ne a wata zantawa da ya yi da shugaba Francois Hollande ta wayar tarho a jiya Juma'a, inda shugaba Obaman ya jaddada kudurinsa na tallafawa wajen ganin an magance aiyyukan ta'addacin a Mali din da kuma arewacin Afrika baki daya.
Baya ga batun ta'addanci a Mali da wasu kasashen arewacin Afrika, shagabannin biyu har wa yau sun tattauna dangane da halin da al'ummar Siriya ke ciki sakamakon yakin da ake tsakanin gwamnati da 'yan adawa inda shugabannin biyu su ka ce za su agazawa 'yan Siriya wajen ganin an samu sauyi a kasar.
Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Saleh Umar Saleh