Obama zai bayyana shirinsa kan mayakan IS
September 8, 2014Talla
Shugaban Amirka Barack Obama zai fara bayyana shirin sa na kawo karshen hare-haren kungiyar IS da ayyukansu ke kara tsamari a Iraki da kasar Syria.
Shugaban zai bayyana wadannan tsare-tsare na shi ne bayan ganawar sa da bangarori biyu na 'yan majalisa a fadar White House a ranar Talata, sannan ya gudanar da jawabi a ranar Laraba gabanin shirye-shirye na tunawa da ranar 11 ga watan Satimba da aka kai wa Amirkan harin ta'addanci a shekarar 2001.
Su dai mambobin majalisar na muradin ganin shugaba Obama ya zayyana irin ayyukan da ya ke son cimmawa kan mayakan na IS.
Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Mohammad Nasiru Awal