1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Odinga: Babu raba madafun iko a Kenya

Yusuf Bala Nayaya
September 3, 2017

Dukkanin bangarorin biyu dai na masu mulki da bangaren adawa a siyasar kasar sun ja daga a shirin fita sake fafatawa a zabe.

Kenia nach der Annulierung der Präsidentenwahl | Raila Odinga
Hoto: picture alliance/AP Photo/B. Curtis

Jagoran adawa a kasar KenyaRaila Odinga ya bayyana cewa ba zai shiga shirin raba madafun iko ba da gwamnatin da ke mulki a kasar yanzu. Odinga ya bayyana haka ne a wannan rana ta Lahadi kwanaki biyu bayan da kotun koli ta soke nasarar da Shugaba Uhuru Kenyatta ya yi a zaben watan Agusta ta kuma bada umarni na a sake zabe cikin kwanaki 60.

Dukkanin bangarorin biyu dai sun ja daga a shirin fita sake fafatawa a zabe inda za a sake gwarawa tsakanin Uhuru Kenyatta dan shekaru 55 da jagoran adawa Odinga dan shekaru 72, dukkanin bangarori biyun dai sun shiga yanayi na ci gaba da karta kasa.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW