'Yan cirani sun awana shekara a Hamada Tenere
April 2, 2020Talla
Hukumar ta OIM ta ce yanzu haka ta killace 'yan ciranin har tsawon makwanni biyu domin tantance ko suna dauke da cutar Coronavirus. 'Yan ciranin wadanda suka galabaita cikin hamada an ganosu tun makwannin biyu da suka wuce cikin hamadar. Daga cikinsu 104 'yan Najeriya, 53 'yan Ghana, sai 34 'yan Burkina Faso har da jariri a ciki a kan hanyarsu ta zuwa Turai ta barauniyar hanya.