Mace za ta jagoranci kungiyar kasuwanci ta duniya
February 15, 2021
Talla
Watanni uku bayan da tsohon shugaban Amirka Donald Trump ya soke bukatar nada ta aka tabbatar mata da wannan matsayi. Shugabar mai shekaru 66, za ta fara aiki a farkon watan Maris na tsawon shekaru biyar, ta kuma ce akwai bukatar karfafa kungiyar kasuwanci ta duniya da zai farfado da tattalin arzikin duniya da ke cikin masassarar annobar corona.
Kungiyar Tarayyar Turai Eu ta marabci tabbatar da Ngozi Okonjo-Iweala a matsayin sabuwar shugabar kungiyar kasuwanci ta duniya, yayin da sabuwar gwamnatin Amirka ta ce a shirye take ta yi aiki da ita domin kaiwa ga ci.