1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka za ta karbi bakuncin Scholz

Lateefa Mustapha Ja'afar
April 28, 2023

A makon gobe ne shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz zai fara wata ziyarar aiki a Afirka karo na biyu tun bayan da ya zama shugaban gwamnati, inda zai ziyarci kasashen Habasha da Kenya.

Jamus | Olaf Scholz Ziyara | Afrika
Shugaban gwamnatin Jamus Olaf ScholzHoto: Michael Kappeler/dpa/picture alliance

Kakakin fadar gwamnati Christiane Hoffmann ce ta bayyana hakan, inda ta ce shugaban gwamnatin Jamus din Olaf Scholz zai kasance a Afirka daga ranar hudu zuwa shida ga watan Mayu mai zuwa. Ziyarar ta Scholz dai, za ta mayar da hankali ne a kan yaki da yunwa da sauyin yanayi da hadin kan tattalin arziki da wanzar da zaman lafiya da sasanta rikici kamar wanda a yanzu haka ake fama da shi a Sudan. Yakin basasar da aka kwashe tsawon shekaru biyu ana gwabzawa a yankin Tigray na Habasha dai, ya yi sanadiyya mutuwar daruruwan mutane kafin a kai ga kawo karshensa bayan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a watan Nuwambar bara.