1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Olaf Scholz ya fasa kai ziyara a Ukraine

Abdourahamane Hassane
April 13, 2022

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Cholz ya ce ya fasa kai ziyara a birnin Kiev na Ukraine, wanda aka shirya a da zai je don bai wa kasar agajin manyan makamai na yaki.

Großbritannien | Bundeskanzler Olaf Schoz trifft Boris Johnson in London
Hoto: BEN STANSALL/Pool/AFP

Cholz ya ce ya ci tuwon fashi ne a kan tafiyar bayan da shugaba Volodymyr Zelensky ya ki amincewa da ziyarar shugaban kasar na Jamus Shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier a Ukraine. Shugaban na Jamus da ke ziyara a  birnin Warsaw na Poland ya so tare da shugabannin kasashen yankin Balkans su  kai ziyara a Kiev amma shugaban kasar Ukraine ya ki amincewa. Saboda zargin da yayi masa na kawo cikas wajen shigar Ukraine cikin kungiyar tarrayar Turai a lokacin da yake rike da matsayin ministan harkokin wajen Jamus da kuma kusancinsa da Rasha.