1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan za ta shiga tsakanin a rikicin Sudan ta Kudu

Abdourahamane Hassane
June 6, 2018

Shugaba Omar Al Baschir na Sudan ya yi tayin shiga tsakanin a rikicin da ake yi a Sudan ta Kudu tsakanin shugaba Salva Kiir da jagoran 'yan tawaye Riek Machar.

Waffenruhe in Somalia ausgehandelt Omar al Baschir Präsident Sudan
Hoto: AP

Al Baschir ya ce a shirye yake ya kira wani taro da zai hada shugaba Salva Kiir da Riek Machar domin tattaunawa don yin sulhu. Wannan yunkuri na zuwa ne bayan da MDD ta gargadi sasan biyu da su samu famitar juna kafin nan da karshen wannan wata ko kuma majalisar ta dauki matakan hukuntasu. A shekara ta 2011 Sudan ta Kudu ta samu 'yancin kai kafin daga bisani a shekara ta 2013 kasar ta shiga yakin basasa. Sakamakon yadda shugaba Salva Kiir ya zargi tsohon firaministansa Riek Machar da yunkurin kifar da gwamnatinsa.