Isra'ila ta hana saukar jirage kan Omicron
November 28, 2021Isra'ilan ce kasa ta farko da ta dauki irin wannan mataki tun bayan da aka gano samfurin Omicron din a ranar Larabar da ta gabata a Afirka ta Kudu.
Hukumomin kasar sun ce sun yi haka ne saboda a yanzu sun kaddara cewa samfurin coronar da ake zullumin zai bijire wa rigakafi ya bazu a kusan kowace kasa ta duniya. Firaminista Naftali Bennett ya ce rufe sufurin saman zai gudana na makonni biyu, inda ake sa ran kafin lokacin masana kimiyya sun samu cikakken bayani kan ita wannan cuta da aka ce ta fi sauran nau'ikan corona irinsu Delta da Alpha saurin yaduwa.
Isra'ila dai ta riga ta samu mutum guda da ke dauke sabon nau'in na corona tun kafin sabuwar dokar da ta sanya. Kawo Lahadin nan Omicron din ta bulla a kasashen Turai daban-daban. Babban likitan Amirka Dr. Anthony Fauci ya ce ba zai yi mamaki ba idan su ma cutar ta rika ta bazu a kasar.