1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Lafiya

Moroko ta hana jiragen saman fasinja

Lateefa Mustapha Ja'afar
December 24, 2021

Mahkuntan Moroko sun kara wa'adin hana jiragen kasashen ketare tashi da sauka a kasarsu zuwa karshen watan Janairun da ke tafe.

USA Symbolbild Flugzeug
Fasinjojin da ke tafiye-tafiye a jiragen sama na fuskantar kalubale saboda omicronHoto: Steve Parsons/PA Wire/empics/picture alliance

Moroko dai ta dauki wannan matakin ne, sakamkon sabon nau'in corona na omicron da ke yaduwa tamkar wutar daji a duniya. Hukumar kula da filayen jiragen sama ta kasar ce tabayyana hakan, inda ta ce ta dakatar da duk wani jirgin fasinja na kasa da kasa da zai sauka ko kuma ya tashi daga kasar har sai nan da ranar 31 ga watan Janairun shekara ta 2022 da ke tafe. Mahukuntan na Rabat sun fara sanya wannan dokar ne a karshen watan Nuwambar da ya gabata, inda a baya suka shirya dage ta a ranar 31 ga wannan wata na Disamba da muke ciki. Sai dai kuma sun amince da bai wa jiragen da ke zuwa domin debe 'yan kasarsu daga kasar, damar kwashe al'ummominsu.