1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Zimbabwe na samun karuwar masu Covid-19

December 3, 2021

Bayanan da hukumomin Zimbabwe suka fitar a Jumma'ar nan na cewa mutum sama da 1000 ya kamu da corona a cikin sa'o'i 24 da suka gabata, sabanin mutane 20 da ake samu a rana a makonni biyun da suka gabata.

Simbabwe Präsidentschaftswahl Emmerson Mnangagwa erklärter Wahlsieger
Hoto: Getty Images/D. Kitwood

Ministan lafayar kasar Constantino Chiwenga ya ce Zimbabwe na cikin yanayi mai hatsari a kan batun corona. Rahotannin da ke shigo mana yanzu-yanzun nan na cewa Zimbabwen ta samu masu dauke da corona samfurin Omicron guda 5o kawo yammacin wannan Jumma'a.

Kasar dai na cikin kasashen kudancin Afirka da manyan kasashen duniya suka yanke sufurin sama a tsakaninsu da su biyo bayan bullar  da Omicron mai ban tsoro ya yi a Afirka ta Kudu. Sai dai hukumomin Zimbabwe sun kakaba sabbin dokoki masu tsauri don shawo kan lamarin.