1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

OPEC za ta fara fidda gangar mai 400,000

Abdul-raheem Hassan
January 4, 2022

Kungiyar kasashe masu arzikin man fetur a duniya wato OPEC da sauran kasashen da ke hako mai, sun jaddada aniyar su na maido da raguwa adadin man fetur da aka rage fitarwa saboda annobar corona.

Bahrain Erdoelfoerderung
Hoto: PantherMedia/Anna Opoleva

Kungiyar na fatan cimma wannan mataki ne bayan la'akari da yawan bukatar man fetur a duniya saboda yawan tafiye-tayfiye, duk da barazanar sabon nau'un corona omicron ke yi na saurin yaduwa a kasashe daban-daban.

Akwai yiyuwar daga watan Febrairu na shekarar 2022, kungiyar OPEC za ta kara yawan adadin man da ta ke fitarwa da sauran aksashen mambobin kungiyar zuwa ganga  400,000 a kowace rana.