1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Tarihin zababbiyar mataimakiyar shugabar Ghana

Abdullahi Tanko Bala SB
December 10, 2024

Farfesa Jane Naana Opoku-Agyemang ta kafa tarihi inda ta zama mace ta farko da aka zaba mataimakiyar shugabar kasar Ghana

Farfesa Jane Naana Opoku-Agyemang zababbiyar mataimakiyar shugabar Ghana
Farfesa Jane Naana Opoku-Agyemang zababbiyar mataimakiyar shugabar GhanaHoto: Zohra Bensemra/REUTERS

A tafiyar dimukuradiyyar da cigaban mata a siyasar Ghana, Farfesa Jane Naana Opoku-Agyemang ta kafa tarihi inda ta zama mace ta farko mataimakiyar shugabar kasa, a karkashin inuwar babbar Jam'iyyar NDC. Tsayar da ita takarar mataimakiyar shugaban kasa ga John Dramani Mahama a zaben 2024 ya kasance zakaran gwajin dafi a tarihin siyasar Ghana da ma yankin yammacin Afirka baki daya.

Takarar Farfesa Opoku-Agyemang wani muhimmin mataki ne wajen daidaita wakilcin mata a siyasar Ghana, musamman a bangaren mukamai na shugabanci. Za ta bayar da gudunmawa matuka bisa la'akari da kwarewarta a fannin Ilmi da fahimta ta gudanar da sha'anin mulki da kuma kasancewa mace ta farko da ta sami daukaka da gogewa a aikin gwamnati.

Karin Bayani: Hukumar zaben Ghana ta bayyana sakamakon zaben kasar

Farfesa Jane Naana Opoku-Agyemang zababbiyar mataimakiyar shugabar GhanaHoto: Fatemeh Bahrami/AA/picture alliance

An haifi Jane Naana Opoku-Agyemang a ranar 22 ga watan Nuwamba, 1951 a gundumar tsakiyar Ghana, ta yi karatunta a Ghana kafin ta fita kasar waje don karo Ilmi. Ta kammala digirinta na farko a Jami'ar Cape Coast a Ghana a fannin Turanci da tarihi, ta yi digiri na biyu a Jami'ar Ghana, daga bisani ta tafi Jami'ar London inda ta yi digirin digigir a dai fannin Turanci. Kafin ta shiga fagen siyasa Farfesa Opoku-Agyemang ta yi aiki a matsayin babbar malama mai koyarwa a Jami'ar Cape Coast, ta bayar da gudunmawa wajen ci gaban Ilmi a Ghana.

Ginshikin da ta samu na Ilmi ya kafa mata tushen nasara da kwazo a rayuwarta inda ta zama a bar koyi na ci gaban mata a fannin Ilmi.

A shekarar 2012 an nada ta mukamin ministar Ilmi a gwamnatin John Dramani Mahama, abin da ya zama tushen daukakarta a rayuwa. A matsayin ministar Ilmi ta jagoranci garambawul da dama na bunkasa ingancin Ilmi a Ghana musamman a matakan sakandare da manyan matakan Ilmi mai zurfi da daidaita tazara da kuma damammakin Ilmi a tsakanin maza da mata.

Hotunan John Mahama zababben shugaban kasar Ghana da Farfesa Jane Naana Opoku-Agyemang zababbiyar mataimakiyarsaHoto: NIPAH DENNIS/AFP

Farfesa Opoku-Agyemang ta fara gwagwarmayar siyasa daga lokain da ta shiga Jam'iyyar NDC, a matsayin fitacciyar 'yar Jam'iyya, ta yi fice wajen gwagwarmayar shigar da mata cikin al'amuran shugabanci a tsakanin al'umma a Ghana. A tsawon rayuwarta ta siyasa, Farfesa Opoku-Agyemang ta jajirce wajen adalci a zamantakewa da ganin ana damawa da kowa. Matsayinta kan hakkin mata da adalci a tsakanin al'umma da kawo gyara kan sha'anin Ilmi sun daga likafarta a matsayin gwarzuwa a fagen siyasar Ghana.

Komai baya rasa kalubale, maza su ne suka yi kaka-gida a fagen siyasar Ghana, hakan kuma ya yi gagarumin tasiri a cikin al'ada tare da yin shamaki ga matan wajen cimma babban matsayi na mukami. Sai dai duk da wannan kalubale takarar Farfesa Opoku-Agyemang ta haifar da muhimin muhawara a game da wakilcin mata da rawar su a fagen siyasa baki daya.

Masu zane a Ghana na murnaHoto: Misper Apawu/AP/picture alliance

A yanayin siyasa a yammacin Afirka kuwa, zaben ta a matsayin mataimakiyar shugabar kasa, muhimmin matakin ci gaba ne wajen kawar da al'adu masu sarkakakiya game da yadda ake kallon mata a siyasa. Zabarta ya nuna mata suna iya rike kowane irin mukami matukar suna da gogewa da kwarewa da kuma kwazon da ake bukata don cigaban kasa.

Daukakar da ta samu daga malamar makaranta zuwa mataimakiyar shugabar kasa, ya kara wa mata kaimi a Ghana da sauran sassa na Afirka wanda ke nuna cewa da kwakkwarar kudiri da kuma goyon baya, mata na iya kafa tarihi da bayar da gudunmawa mai ma'ana ga ci gaban kasashensu. A matsayin mataimakiyar shugabar kasa, Farfesa Opoku-Agyemang ta kafa tarihi a siyasar Ghana. Ko da za ta rike wani mukami a nan gaba, ko kuma za ta ci gaba da yin riko da wasu abubuwan da take gani masu muhimmanci, tarihin da ta kafa na ja gaba a fagen siyasar mata, zai ci gaba da karfafa gwiwar al'ummar da za su zo a nan gaba.