Bukatar fahimta tsakanin Amirka da Rasha
January 13, 2022Talla
Kungiyar kawancen tsaro da raya cigaba a nahiyar turai OSCE ta na fatan kwantar da hankula a rikicin kan iyaka na kasar Ukraine inda Rasha ta jibge dakarun sojinta masu yawa.
Poland ta fara gabatar da mukala inda ta yi kashedin cewa akwai hadarin barkewar yaki a yankin kasashen kungiyar OSCE kuma lamarin ya yi kamari a wannan karon fiye da sauran lokuta shekaru 30 da suka gabata.
Ministan harkokin wajen Poland Zbigniew Rau ya shaidawa mahalarta taron a babban birnin Austria cewa akwai bukatar tabbatar da hadin kai da fahimtar juna a tsakanin kasashe.