Osinbajo: A maido mana da kudadden sata
July 11, 2017Duk da tsegumi game da dangantaka a tsakanin shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na Rasha Vladimir Putin da ya mamaye taron koli na kasashe 20 masu karfin masana'antu, taron da ya gudana a birnin Hamburg na kasar Jamus bai manta da nahiyar Afirika da ke fama da rikicin ‘yan gudun hijira da kuma tsananin talauci ba. Ko bayan shirin nan da aka yi wa lakabi da ''Compact with Africa'' da kasar Jamus ta shirya a kokarin kwadaitawa shugabannin mahinmancin zuba jari don sake farfado da tattalin arzikin Afirika a kokarin samar da ababe na more rayuwa a nahiyar, akwai kuma batun maido wa Najeriya da sauran kasashen Afirika Miliyoyin daloli da ake zargin wasu sun wawure sun kuma boye a manyan bankunan a kasashen ketaren.
A wata wasikar da mukadashin Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya aike ya zuwa mahalarta taron, ya nemi daukar mataki a cikin gaggawa don maido da makudan kudadden nahiyar domin amfanin al'umma ta nahiyar da ke fuskantar matsanancin rayuwa na talauci. Alkaluma dai sun nuna cewar akwai bukatar samar da ayyukan yi ga mutane fiye da miliyan biyu a shekara guda in har ana son magance matsalar talaucin da ke addabar al'ummar yankin ganin yadda a ke ci gaba da fuskantar karuwar al'umma.
A cewar Dakta Kole Shettima shugaban cibiyar demokaradiya da ke fafutukar tabbatar da mulki na gari a Najeriyar, ya ce wasikar Osinbajon na zama mai tasiri a kokarin da ake na ceto nahiyar daga cikin halin matsatsin da ta sami kanta a yanzu .An kiyasta cewar akalla dalar Amurka Miliyan Dubu 50 ake fitarwa daga kasashen nahiyar ta Africa zuwa kasashe turai ta barauniyar hanya sakamakon kin bin doka ko kuma cin hanci da rashawa da ya adabi yankin, yayin da masu sharhi ke ganin abu mafi sauki da shugabanin za su yi, shi ne su soma dawo da kudadden maimakon mayar da hankali kan magance matsalolin bakin haure da fadan da suke yi da ayyukan ta'addanci ganin talauci ne ya soma haifar da wadannan matsalolin tun a farko. Abun jira a gani na zaman tasiri wannan kiran na maido da kudadden da aka sace don bunkasa tattalin arzikin nahiyar Afirika da zai taimaka wajen magance matsalolin talauci da kwarararr bakin haure a Turai.