1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Ostareliya ta hana yara amfani da kafofin sadarwa na zamani

November 29, 2024

Majalisar dokokin Ostareliya ta amince da kudurin dokar hana yara 'yan kasa da shekara 16 amfani da kafofin sadarwar zamani.

Wasu alamomin kafofin sadarwar zamani
Wasu alamomin kafofin sadarwar zamaniHoto: Dado Ruvic/REUTERS

'Yan majalisun dokokin kasar sun ce haramcin ya shafi kafofi irin su facebook da Instagram da TikTok da Snapchat da Reddit har ma shafin X, amma an yi sassauci kan amfani da wasu shafukan kan binciken ilimi da kiwon lafiya irin su Youtube da Messenger Kids da kuma WhatsApp.

Karin bayani: Ba'asin zargin Facebook da cutar da yara 

Da yake tsokaci kan dokar firaministan Ostareliya Anthony Albanese ya ce dokar za ta bai wa yara kanana kariya daga rudin zuciya, kasancewar soshiyal midiya na mummunar illa ga yara kanana a fadin kasar. Ita ma ministar sadarwar kasar Michelle Rowland ta ce sun shafe watanni suna gudanar da bincike da kuma taba-alli da kwararru kan yadda za a aiwatar da shirin hana yara kanana amfani da shafukan sadarwa na zamani.