Ostareliya ta lashe amanta kan birnin Kudus
October 18, 2022kasar Ostareliya ta yanke shawarar kin amincewa da birnin Kudus a matsayin babban birnin kasar Isra'ila, sakamakon sauya matakin da gwamnatin da ta gabata ta dauka a kan wannan batu. A lokacin da take bayani a birnin Sydney, ministar harkokin wajen kasar Penny Wong ta ce, ya kamata a warware matsayin birnin Kudus ta hanyar shawarwarin zaman lafiya tsakanin Isra'ila da al'ummar Falasdinu, amma ba ta hanyar yanke shawara na bai daya ba.
Gwamnatin da ta gabata ta Scott Morrison ta fuskanci suka a shekara ta 2018, lokacin da ta sanar da amincewa da yammacin birnin Kudus a matsayin babban birnin Isra'ila, bayan wani mataki makamancin wannan da shugaban Amirka na wannan lokaci Donald Trump ya dauka. Isra'ila da Falasdinawa na ikirarin mallakar birnin Kudus, amma galibin kasashen ketare na kauce wa kafa ofisoshin jakadanci a yankin, saboda tsoron makomar tattaunawar zaman lafiya kan matsayin birnin.