Ostareliya za ta kwace fasgon 'yan jihadi
May 26, 2015![Irak Milizen](https://static.dw.com/image/18461597_800.webp)
Kasar Ostareliya ta shirya amincewa da wata doka cikin makonni da ke tafe, da za ta bawa gwamnati karfin iko na karbe takardun zama a kasa da wasu mutane ke da shedar zama a kasashe guda biyu, dokar da za ta yi aiki ne kan wadanda ake zargi da ayyukan ta'addanci koda kuwa ba a same su da laifi ba, kamar yadda Firaministan kasar Tony Abbot ya bayyana a ranar Talatan nan.
Fiye da mutane 100 ne 'yan kasar ta Ostareliya ake zargi da shiga kungiyar mayakan IS a Iraki da Siriya, inda kashi 50 cikin dari na wadan nan mutane ake ganin suna da takardun sheda ne ta zama a kasar ta Ostareliya da wata kasar.
A cewar Firaminsta Abbot kwaskwarimar da za a yi wa wannan dokar zama dan kasa, za ta sanya a hukunta masu goyon bayan kungiyar ta IS da ke ciki da wajen kasar ta Ostareliya, inda za a dauke su tamkar wadanda suka dauki makamai dan yakar kasar ta Ostareliya.