Ostireliya ta nemi afuwan yaran da aka ci zarafinsu
October 22, 2018Talla
A jawabinsa na wannan Litinin a zauren majalisar kasar, Firaminisa Scott Morrison na Ostireliya ya ce a matsayin mu na kasa mun amince da gazawarmu a jan kafa da aka samu na sauraron koken wadanda suka nemi fadin gaskiya kan halin da 'ya'yanmu suka fada a hannun limaman coci ba tare da mun iya ceto su daga wannan bala'i ba.
Wannan na zuwa ne, shekara guda bayan da bincike wata hukuma mai rajin hana cin zarafin yara, ya gano cewa, kashi bakwai cikin dari na malaman katolika sun yi lalata da yara a tsakanin shekarun 1950 da 2010 a kasar. Bayan jawabin ministan, wasu daga cikin wadanda aka ci zarafinsu, sun nuna gamsuwa wasu kuwa sun ce ihu ne kawai bayan hari.