SiyasaTurai
Manyan kasashen duniya sun kara arziki a corona
January 17, 2022Talla
Dukiyar manyan attajiran duniya guda 10 ta rubanya a cikin shekaru biyu da aka yi ana cikin annobar corona. Kungiyar Oxfam mai fafutukar adawa da talauci a duniya ce ta sanar da haka a cikin wani sabon rahoto da fitar a wannan Litinin (17.01.2022).
Gabriela Bucher ita ce shugabar kungiyar ta Oxfam. Ta ce '' Idan da za a karbi dukiyar da attajiran nan suka samu a lokacin corona da za a iya samar wa da duniya gaba daya rigakafin corona tare da biya wa duk wani mara karfi a duniya kudin asibiti.''
Kungiyar ta ce ta fitar da rahotanta a wannan mako domin babban taron duniya kan tattalin arziki na duniya da za a yi ta hanyar bidiyo ya san matakan da zai dauka don kauce wa daukar matakan da za su sanya a kara wa mai karfi, karfi.