1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin bam ya kashe mutane a Islamiyya

Abdullahi Tanko Bala
October 27, 2020

Akalla dalibai takwas ne ciki har da kananan yara suka rasu wasu da dama kuma suka sami raunuka a wani harin bam da ya fashe yayin da dalibai ke tsakiyar karatu a wata makarantar Islamiyya a arewa maso yammacin Pakistan.

Pakistan Anschlag auf eine Religionsschule in Peschawar
Hoto: Abdul Majeed/AFP/Getty Images

Wani jami'in dan sanda a yankin Peshawar da lamarin ya faru Waqar Azim yace mutane fiye da 60 ne suke daukar darussa a lokacin da bam din ya fashe.

Yace wanda ya ajiye bam din a cikin wani kunshin kaya ya fice kafin bam din ya tashi. Dalibai 34 ciki har da malamai biyu suka sami raunuka a harin. Babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin.

Gundumar Peshawar da lamarin ya faru ya yi kaurin suna wajen yawaitar hare hare a pakistan inda masu ikrarin jihadi ke kai hari akan jami'an tsaro.
 

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW