1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Pakistan da Iran sun sasanta

Suleiman Babayo MA
January 22, 2024

Kasashen Iran da Pakistan sun dauki matakin rage zaman tankiya bayan rikicin da aka samu gami da bayyana mayar da jakadu tsakani bayan sakun saka da aka samu.

Iyakar Pakistan da Iran
Iyakar Pakistan da IranHoto: Banaras Khan/AFP/Getty Images

Kasashen Iran da Pakistan sun bayyana mayar da jakadu da aka janye tsakanin kasashen biyu bayan sakun saka da aka samu, sannan kasashen sun amince da matakan rage zaman tankiya da ke tsakanin su, sakamakon harba makamai daga duk bangarorin biyu.

Shi kansa Hossein Amir-Abdollahian ministan harkokin kasashen ketere na Iran ya bayyana shirin kai ziyara zuwa Pakistan a karshen wannan wata na Janairu, sakamakon goron gayyana da ya samu daga takwaransa Jalil Abbas Jilani, kamar yadda wata sanarwa ta tabbatar a wannan Litinin.

A cikin wannan makon jakadun na kasashen Iran da Pakistan za su koma bakin aiki janyewa da aka yi, saboda a makon jiya Iran ta harba makami zuwa cikin Pakistan ita kuma ta mayar da martani, kowanne bangare ya ce ya yi haka ne saboda tsageru masu lebewa suna kai hare-hare tsallaken iyaka.