Harin kunar bakin wake ya hallaka mutane 44 a Pakistan
July 30, 2023Talla
An nufi harin ne kan jam'iyyar Jamiat Ulema al Islami JUI-F party wadda ke cikin kawancen gwamnati karkashin jagorancin wani fitaccen malamin addini.
Ministan lafiya na gundumar Khyber Riaz Anwar ya tabbatar da mutuwar mutane 44 yayin da wasu fiye da 100 suka sami raunuka.
Babu kungiyar da ta dauki alhakin harin kawo yanzu sai dai kungiyar IS ta sha kai hare hare kan Jam'iyyar ta JUI-F a baya bayan nan.