Pakistan: Kotu ta wanke tsohon Firaminista Imran Khan
June 3, 2024Wata kotu a Pakistan a wannan litinin ta sauya hukuncin dauri kan zargin cin amanar kasa da aka yanke wa tsohon Firaministan kasar Imran Khan kamar yadda lauyansa da kuma Jam'iyyarsa suka sanar.
Tsohon Firaministan da tsohon ministansa na harkokin waje Shah Mahmood Qureshi an same su da laifi a shekarar 2022 kan fallasa wasu bayanan sirrin gwamnati wanda jakadan Pakistan a Washinton ya tura Islamabad.
Lauyan Khan Salman Safdar ya ce wannan ita ce babbar tuhuma ta makircin siyasa da aka shirya wa Imran Khan da Shah Mahmood Qureshi da aka yi nasarar murkushewa.
Khan ya yi zargin cewa bayanan wata shaida ce da ke tabbatar da cewa Amurka na shirya makarkashiyar kifar da shi daga kan mulki a shekarar 2022 inda majalisar dokoki ta kada masa kuri'ar yankar kauna.