Pakistan na adawa da shirin Kungiyyar kasashe renon Ingila
November 21, 2007Talla
Pakistan ta yi kira ga ƙungiyyar ƙasashe renon Ingila da ta tsagaita yanke hukuncin dakatar da ita, a matsayin mamba a ƙungiyyar. Kakakin ma´aikatar harkokin wajen ƙasar ya ce tuni sabon faraminista, Mohammadmian Soomro ya buƙaci ƙungiyyar ta Commonwealth tura manzo izuwa ƙasar, don ƙalailaice halin da ake ciki. A gobe Alhamis ne wa´adin da Commonwealth ɗin ta ɗebarwa shugaba Musharraf yake ƙarewa, na ko dai ta cire dokar ta ɓacin data kafa ko kuma ta fuskanci hukuncin dakatarwa. A gobe ne dai ministocin ƙungiyyar na Commonwealth za su gudanar da taro, a babban birnin ƙasar Uganda,wato Kampala don tattauna wannan batu.