1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Pakistan: Shehbaz Sharif ya sake zama Firaminista

March 3, 2024

Majalisar dokokin Pakistan ta zabi Shehbaz Sharif a matsayin Firaministan kasar a wa'adi na biyu. Hakan dai na zuwa ne bayan makonni da gudanar da babban zaben kasar.

Firanministan Pakistan, Shehbaz Sharif
Firanministan Pakistan, Shehbaz Sharif Hoto: K.M. Chaudary/AP Photo/picture alliance

Shehbaz Sharif mai shekaru 72 da haihuwa ya samu nasara ne da kuru'u 201, yayin da dan takara na jam'iyyar tsohon Firanminista Imran Khan da ke daure, Omar Ayub Khan ya ke da kuru'u 92 daga cikin kujerun 336 na majalisar dokokin.

Magoya bayan Imran Khan dai sun nuna kin amincewa da sakamakon, inda suka zargi cewa an tafka magudi a zaben na watan jiya.

Karin bayani: Ana gudanar da zabe a kasar Pakistan 

Bayan shan rantsuwar kama aiki, ana sa ran Shehbaz Sharif ya kara neman rance daga asusun bada lamuni na duniya yayin da wa'adin bashin da ake bin kasar ke karewa a wata mai zuwa.

Kasar Pakistan dai na fama da tsadar rayuwa sakamakon halin masassara da tattalin arzikin kasar ke fuskanta.