1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Rikice-rikiceAsiya

Pakistan ta harba wa Indiya makamai masu linzami

May 10, 2025

Pakistan ta kaddamar da hare-hare ta sama kan kasar Indiya bayan da ta yi ikirarin cewa mahukunta a New Delhi sun kai hari a wasu sansanonin sojanta guda uku a a ranar Juma'a da daddare.

Hoto: Jamil Bhatti/Xinhua/picture alliance

An ji fashe-fashen abubuwa masu hatsari a wasu birane dabam-dabam yayin da al'ummar duniya ke kira da a yi gaggawar samar da maslaha.

Tun da farko, rundunar sojin Indiya ta ce ta harbo wasu jiragen leken asiri na Pakistan a birnin Amritsar a safiyar Asabar, tana sukar abin da ta kira "yunkurin taba muhibbar kasar Indiya da kuma barazanar Paksitan kan rayukan fararen hula."

A cikin bayanin da ya yi, don kare kasarsa kan harba makamai masu linzamin, ministan harkokin wajen Pakistan, Ishaq Dar, ya ce ba su da wani zabi face su mayar da martani ga harin na Indiya, yana zargin New Delhi data'azzara al'amura.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, ya yi magana da Shugaban Sojin Pakistan, Asim Munir, inda ya yi kira ga Pakistan da Indiya da su "nemo hanyoyin sasanta cikin lalama, yana mai cewa Amurka a shirye take wajen fara tattaunawar zaman lafiya domin kauce wa ci gaba da kazancewar rikicin.