1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Pakistan ta kai hare-hare ta sama kan Afghanistan

September 21, 2026

Pakistan ta kai sabbin hare-hare ta sama kan Afghanistan, tana mai cewa tana farautar mayakan da ke kai mata hare-hare daga ketare.

Afghanistan Kabul 2026 | Löscharbeiten nach pakistanischem Luftangriff
Hoto: Wakil Kohsar/AFP/Getty Images

Pakistan ta kai hare-hare ta sama kan wasu yankunan arewa maso gabashin Afghanistan da ke kan iyakar kasashen biyu, tana mai cewa ta kai farmakin ne kan kungiyoyin da take zargi da kai hari kan wani sansanin 'yan sanda a makon jiya.

Ma'aikatar yada labaran Pakistan ta ce an kashe mayaka 28 a hare-haren. Islamabad na zargin kungiyar TTP ta Taliban Pakistan da amfani da maboyarta a Afghanistan wajen shirya hare-hare a Pakistan.

Sai dai gwamnatin Taliban ta Afghanistan ta musanta zargin, tana mai cewa hare-haren Pakistan sun keta hurumin kasar tare da kashe fararen hula uku.

Ba a iya tabbatar da alkaluman wadanda suka mutu da bangarorin biyu suka bayar ba. A halin yanzu, akasarin mashigar kan iyakar kasashen biyu na ci gaba da kasancewa a rufe.

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW