1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Pakistan ta nesanta kanta daga tukwicin kisa

September 23, 2012

Pakistan ta soki lamirin alkawarin tukwici da wani minista a gwamnatin ya yi ga duk wanda ya kashe mutumin da shirya fim din batanci ga addinin Islama.

A supporter of the religious party Idara Sirat-e-Mustaqeem holds a placard during a rally with some 600 other protesters against an anti-Islam film made in the U.S. mocking Prophet Mohammad, in Lahore September 23, 2012. A Pakistani minister offered $100,000 on Saturday to anyone who kills the maker of an online video which insults Islam, as sporadic protests rumbled on across parts of the Muslim world. REUTERS/Mohsin Raza (PAKISTAN - Tags: POLITICS CIVIL UNREST RELIGION)
Hoto: Reuters

Gwamnatin Pakistan ta nesanta kanta daga tukwicin da wani minista a gwamnati ya yi alkawarin bayarwa ga dukkan wanda ya kashe mutumin da ya shirya fim din nan da ya yi batanci ga addinin musulunci. Wani mai magana da yawun Firaministan kasar Raja Pervez Ashraf yace babu ruwan gwamnatin da abin da ministan ya yi kuma ba manufa ce ta gwamnatin Pakistan ba. A ranar Asabar ce dai ministan sufurin jiragen kasa Ghulam Ahmed Bilour ya yi alkawarin bada tukwicin dala dubu 100 daga aljihunsa ga duk wanda ya kashe mutumin da ya shirya fim din nan da ya ci zarafin addinin musulunci da kuma manzon Allah, yana mai kira ga kungiyar Taliban dana Al-Ka'ida su shiga wannan muhimmin aiki na sadaukarwa.

Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Umaru Aliyu