1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Pakistan ta yanke wa Shakil Afridi hukuncin dauri na shekaru 33

May 25, 2012

Majalisar dattawan Amirka ta tsai da shawarar rage kudin ta take bayarwa a matsayin tallafi ga Pakistan domin nuna fushinta da hukuncin da aka anke wa liktan da ya tono mabuyan bin Laden

This photo taken on July 9, 2010 shows Pakistani doctor Shakil Afridi taken in Pakistani tribal area of Jamrud in Khyber region. Pakistani doctor Afridi, who helped the U. S. track down Osama bin Laden, was sentenced to 33 years in prison on Wednesday for conspiring against the state, officials said. (Foto:Qazi Rauf/AP/dapd)
Shakil AfridiHoto: dapd

A matsayin martaninta ga hukuncin dauri a gidan yari na shekaru 33 da aka yanke wa likitan da ya taimaka wajen gano mabuyar Bin Laden a kasar Pakistan, majalisar dattawan Amirka ta ce za ta rage tallafin kudin da ta ke bai wa kasar. Komitin kudin majalisar ya tsai da shawarar rage taimakon kudin daga dala miliyan dubu zuwa miliyan 33. Kenan kasar ta Pakistan za ta rinka samun dala miliyan daya a kowace shekara bisa hukuncin cin amanar kasa da aka yanke wa Shakil Afridi wanda ma'aikatar leken asirin Amirka CIA ta ba wa kwangilar gudanar da shirin allurar riga kafi a garin Abottabad domin gano kwayoyin halitta na jini da za su kai ga gano mabuyar bin Laden. 'Yan majalisar dattawan Amirka sun yi kira da a yi wa likitan afuwa a kuma sake shi ba da wani sharadi ba.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Usman Shehu Usman