Pakistan ta yi gwajin Makami mai linzami
April 25, 2012Pakistan ta samu nasarar gwajin makaminta mai linzami mai matsakaicin zango, ƙasa da mako guda bayan da Indiya ta yi gwajin nata mai dogon zango. Rundunar sojin ƙasar dai bata sanar da takamammen nisan da makamin zai iya isa ba, sai dai general Talat Masood, masanazarci kan lamuran tsaro ya faɗa wa kamfanin dillancin labaru na AFP cewar zai iya tafiyar nisan km 2,500 zuwa 3,000, batu dake nuni da cewar zai iya isa Indiya dake makwabtaka, wadda kuma ke zama babbar abokiyar gabar Pakistan. A ranar Alhamis da ta gabata ne dai Indiya ta yi gwajin makaminta mai linzami mai nisan zango mai suna Agni V,wanda zai iya lalata makamin Nukiliya tonne guda a ko'ina cikin ƙasar China. A wannan larabar ce dai Pakistan ta sanar da gwajin makamin nata na Haft 4 Shaheen, mai nisan matsakaicin zango a cewar sanarwar rundunar sojin ƙasar. Indiya da Pakistan da suka gwabza yaki har sau uku tun bayan samun 'yancin kai daga Britaniya a shekara ta 1947, sun sha gwajin makamai masu linzami, da ke zama tankar tauna tsakuwa ne don aya ta ji tsoro, tun bayan da dukkanninsu suka nuna cewar zasu iya kera makaman ƙare dangi na Nukiliya a shekara ta 1998.
Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe