1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shehbaz Sharif ya zama sabon firaministan Pakistan

Suleiman Babayo ATB
April 11, 2022

Shehbaz Sharif jagoran 'yan adawa na kasar Pakistan ya zaman sabon firaminista bayan kada kuri'a a majalisar dokokin inda ya maye gurbin tsohon Firamnista Imran Khan da majalisa ta kada masa kuri'ar yanke kauna.

Shahbaz Sharif
Hoto: Anjum Naveed/AP/picture alliance

Majalisar dokokin Pakistan ta zabi Mohammad Shahbaz Sharif jagoran 'yan adawa a matsayin sabon firamnista wanda ya maye gurbin Imran Khan da majalisar dokokin ta tsage a karshen mako.

Sabon Firaminista Mohammad Shahbaz Sharif yana da jan aiki farfado da tattalin arzikin kasar da samar da ci-gaban da ake bukata. Shi dai Shehbaz Sharif ya kasance dan uwa ga tsohon Firamini Nawaz Sharif wanda sau uku yana rike mukamun na firaminista.

Sharif ya lashe zaben zama firaministan kasar ta Pakistan da kuri'un 'yan majalisar dokoki 174 daga cikin 'yan majalisa 342.