Pakistan ta yi tayin sasanta Iran da Saudiyya
January 20, 2016Firaministan kasar Pakistan Nawaz Sharif, ya yi tayin sasanta sabanin da aka samu tsakanin kasar Iran da Saudiyya. Bisa wannan dalilin Sharif ya yi wata ganawa da Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani jiya talata a Tehran, gabanin hakan a shekaran jiya suka gana da Sarki Salman na Saudiya a Riyad. To ko wadannen dalilai ne suka sa Pakistan shiga sasanta kasashen biyu masu gaba da juna a yankin gabas ta tsakiya.
Kasar Pakistan dai ko da yake akasarin al'ummarta mabiya Sunni ne, amma 'yan Shi'a suma suna da karfi. Kuma ana samun fito na fito tsakanin wadannan bangarori a Pakistan. Bayan hari kan ofishin jakadancin Saudiya da ya biyo bayan kashe wani kusa a mabiyan Shi'an Saudiya, daruruwan mutane a Pakistan suka bore na yin Allah wadai da Iran.
"Iran na kawo cikas a bangaren musuluncin duniya. Suna yin shisshige a al'amuran wasu kasashe. Suna jawo tashin hankali da kiyayya tsakanin Musulmai"
'Yan kilo mita kadan a gefen akwai wasu daruruwan 'yan Shi'a marasa rinjaye a Pakistan, suma suna tasu zanga-zangar goyon bayan Iran suna Allah wadai da kisan Sheikh Nimr wanda Saudiyya ta yi. Wannan ya nuna cewa Pakistan na tsakiya kan wadannan masu bin mazhabobi mabambanta. Ko da yake yan shi'a tsirarune, amma an yi kiyasin sun kai kashi 20 cikin dari na yawan al'ummar Pakistan, wato sun kai kimanin mutane miliyan 40 a kasar.
Dangantakar Pakistan da kasashen Saudiyya da iran
Dama dai an yi shekaru ana samun zubda jini tsakanin Shi'a da Sunna a Pakistan, don haka rikicin Iran da Saudiyya dama matsalace da aka saba da ita a cikin gidan Pakistan. Abin da kuma Tahir Malik Farfesa a Jami'ar kasar ta Pakistan ya tabbatar.
"Iran da Saudiyya duk suna da mahimmanci ga Pakistan, domin a yayinda suke da mabiya Sunni kamar Saudiyya haka kuma Iran babbar kasa ce mai makobtaka da Pakistan. Huldar kasashen wajenmu dole ta yi abin da zai amfani kasarmu, ba wai biyan bukatar wani tafarki ko kungiya ba"
Ribar Pakistan ga sasanta Saudiyya da Iran
Bisa wadannan dalillai shiga tsakanin don dinke barakar Iran da Saudiyya, zai yi nasarar yafa ruwa ga bambancin darika da ake fama da shi a cikin gidan Pakistan.
A gefe guda Pakistan na bukatar hulda da dukkan kasashen biyu, misali baya ga dimbin mai da kasar ke sayowa daga Saudiyya, akwai kamfanonin Pakistan da yawa da ke aiki cikin Saudiyya, kana Saudiyyar ce ke biyan kudin tafiyar da makarantu kimanin dubu 20 na koyar da kur'ani a Pakistan.
Amma a daya hannun kasar Iran wadda aka kawo karshen takunkumi da ke kanta, za ta iya zama babbar kasar da za ta bai wa Pakistan iskar gas, inda sama da shekaru 15 aka fara batun shinfida bututun iskar gas tsakanin kasashen biyu. Kasar Pakistan na fiskatar matsalar karancin makamashi, don haka yake ma'ana idan ta shiga sasanta manyan kawayenta, makobciya Iran da babbar kawa Saudiyya.