1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Pakistan ta soki Amirka a Zauren MDD

September 25, 2021

Firaministan Pakistan Imran Khan ya yi yunkurin nuna Amirka a matsayin kasar da ba ta da dattaku.

Pakistan Islamabad | Imran Khan, Premierminister
Hoto: Saiyna Bashir/REUTERS

A yayin jawabinsa ga Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya a ranar Juma'ar da ta gabata, Khan ya ce Pakistan ta dandana rashin godiya da rashin tsayayyar maganar da Amirka ke nuna wa kasashen duniya.

Firaministan Khan ya ce wasu 'yan siyasar Amirka da Turai na zargin Pakistan da hannu a Afghanistan. Sai dai ya ce tun daga harin da aka kai wa Amirka na ranar 9 ga watan Satumba, Pakistan ta fara bakin jini saboda kawancen da ta yi da Amirka. Ya ce a karshe 'yan Pakistan dubu 80 ne suka rasa rayukansu a sakamakon tallafa wa Amirka da kasar ta yi.

''Dalilin wahalar da muka sha shi ne kawancen da muka yi da Amirka a yakin Afghanistan. Ya kamata ace an gode mana amma sai ga shi ana zargin mu da lalacewar al'mura a Afghanistan.'' inji Khan

To amma duk da wannan bayanin nasa, da yawan mutanen Afghanistan sun zargi Pakistan da taimaka wa Taliban murmurar karfin da ta kwace iko da kasar.