Pakistan za ta dauki mataki kan yaki da ta'addanci
December 25, 2014Talla
Firaministan kasar Pakistan Nawaz Sharif ya bayyana kafa kotun soji wadda za ta yi shari'ar wadanda ake zargi da ayyukan ta'addanci, domin dakile 'yan kungiyar Taliban masu kai hare-hare.
Kusan duk shugabannin jam'iyyun kasar da shugabannin hukumomin tsaro suka gana a Islamabad babban birnin kasar domin shirya hanyoyin tunkarar 'yan ta'adda bayan harin da aka kai wata makaranta abin da ya yi sanadiyar hallaka fiye da mutane 140 gabali dalibai. Masu za su tabbatar da dakile ta'addanci, da tsattsauran ra'ayi.
Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Zainab Mohammed Abubakar