Palasɗinawa sun miƙa wuya ga buƙatun Isra'ila
January 25, 2011A ƙarƙashin yarjejeniyar dai shugaban Palasɗinawa Mahmud Abbas ya ba da kai bori ya hau ga buƙatun Isra'ila fiye da yadda ake zato. Fito da wannan kundin da aka yi wani babban abin kunya ne ga mahukuntan Palasɗinawa da ma Isra'ilar baki ɗaya.
Isra'ila dai ta sha iƙirarin cewar wai ba ta da abokan tattaunawa na sulhu, a duk lokacin da jami'an siyasar ƙasar suka sadu da takwarorinsu daga nahiyar Turai ko Amirka, domin bayyana dalilin rashin samun wani ci gaba a tattaunawa da Palasɗinawa.
Tattaunawar sulhun ba a yinsu da zuciya ɗaya
Amma fa a haƙiƙa kundin da tashar Aljazeera da jaridar Guardian ta Britaniya suka fitar, yana mai yin nuni ne da akasin hakan. Bisa ga dukkan alamu Palasɗinawan ne dai ba su da abokan tattaunawa na sulhu. Domin kuwa duk da ba da kai bori ya hau da suka yi, wakilan Isra'ila sun sa ƙafa sun yi fatali da lamarin. Domin kuwa hatta gwamnatin Olmert da Livni, wadda ƙasashen ƙetare ke wa kallon wata gwamnati mai sassaucin manufofi, ta ƙi ta nuna gamsuwarta da tayin Palasɗinawan, alhali kuwa shirin Palasɗinawan na janyewa daga haƙƙinsu tamkar dai kisan kai ne da kai. Domin nkuwa sun bayyana shirinsu na kakkaɓe hannu daga buƘƙatarsu ta janyewar Isra'ila zuwa zirin iyaka na shekara ta 1969. A baya ga haka sun yi tayin cimma wata manufa mai sassauci dangane da tsofon birnin Ƙudus da amincewa da matsugunan yahudawan da aka giggina a yankunan Palasɗinawa dake gabacin Ƙudus.
Isra'ila ba ta gamsu da tayin Palasɗinawa ba
Amma fa dukkan wannan bai gamsar da wakilan Isra'ila ba, inda suka dage akan cewar lalle sai Palasɗinawan sun janye daga buƙatarsu ta rushe matsugunan Yahudawa a yankin yamma da kogin Jordan. Amma fa hakan na ma'ana ne cewar Palasɗinawan ba zasu samu wata tsayyar ƙasa mai dunƙulalliyar haraba ba. Kazalika wakilan Isra'ilar sun ƙi su janye daga buƙatunsu ko da gwargwadon taki ɗaya ne. A taƙaice kundin da Aljazeera ta fallasa yana mai ba da gaskiya ne ga masu saka ayar tambaya game da shirin zaman lafiya daga ɓangaren Isra'ila. Sai dai kuma ba kawai Isra'ila ce ta ji kunya game da fallasa wannan kundi ba, hatta su kansu shuagabannin Palasɗinawa martabarsu ta zube, saboda ba su wakilci maslahar al'umarsu daidai yadda ya kamata ba. A asurce suka miƙa wuya akan haƙƙin Palasɗinawa. Kamar dai yadda aka saba gani tun bayan shawarwarin zaman lafiya na Oslo, shuagabannin sun sake mayar da kansu tamkar 'yan kanzagin daular mamaye ta Isra'ila. Sun sa ido suna masu kallon yadda Isra'ila ta riƙa cin karenta babu babbaka a zirin Gaza da kuma yadda gwamnatin Isra'ilar tayi shekara da shekaru tana mai fatali da tsarin yarjeniyoyi na ƙasa da ƙasa.
Mawallafi: Bettina Marx/Ahmad Tijani Lawal
Edita: Usman Shehu Usman