Italiya ta yi sabon Firaminista
December 11, 2016Talla
Shi dai sabon Firaministan na Italiya Gentiloni mai shekaru 62 a duniya, ana yi masa kallon na kusa da tsohon Firaminista Matteo Renzi mai murabus, wanda kuma jam'iyyarsa ta (DP) "Demokaratique Parti " ta saka shi a sahun gaba daga cikin wadanda take son su karbi wannan mukami. A jawabinsa na farko bayan bashi wannan mukami, sabon Firaministan na Italiya cewa ya yi:
"Ina mai imanin da bukatun da ke garemu cikin gaggawa na bai wa kasar Italiya sabuwar gwamnati mai cikeken iko, wadda za ta bai wa al'ummar kasar kwarin gwiwa da kuma fuskantar manyan kalubale da suka hada da hulda ta kasa da kasa, tattalin arziki da kuma al'umma kuma dukkannin su cikin daukar niya da aiki tukuru."