1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Papa Roma ya yi ikira ga samad da zaman lafiya a Iraqi da yankin Gabas Ta Tsakiya.

July 2, 2006

Shugaban ɗariƙar Katolika, Papa Roma Benedikt na 16, ya nuna matuƙar damuwarsa ga tashe-tashen hankulllan da ke ta ƙara yaɗuwa a Iraqi da kuma Gabas Ta Tsakiya. Da yake huɗuba ga dubban mabiya ɗariƙarsa, a wani taron ibada a dandalin St. Peters a daular Vatican yau, Papa Roman ya yi kira ga zaman cuɗe-in cuɗe ka cikin lumana tsakanin al’ummomin wannan yankin. Ya roƙi Allah ya sassauta zukatan duk masu tsatsaurar ra’ayi a yankin, ko daga wane ɓangare kuma suke, don su fahimci cewa dukkansu ’yan uwan juna ne.

Tun makon da ya gabata ne dai Isra’ila ta tsananta ɗaukin sojin da take yi a zirin Gaza, yayin da mayaƙan Ƙungiyar Hamas suka cafke sojanta ɗaya a wani harin da suka kai wa rukuninsa a kan iyakar Gazan da ƙasar bani Yahudun. Rahotanni dai sun ce jiragen saman yaƙin Isra’ilan sun jefa bamabamai kan ofishin Firamiyan Falasɗinawan Ismail Haniyeh a birnin Gaza, inda masu kare lafiyarsa guda uku suka rasa rayuukansu.