1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Paparoma na ziyara a Indonisiya

September 3, 2024

Jagoran Kiristoci mabiya darikar Katolika na Duniya Paparoma Francis ya sauka a birnin Jakarta na kasar Indonisiya domin fara shirinsa na ziyara mai girma da bai taba yin irinta ba.

Indonesien | Besuch Papst Franziskus in Jakarta
Hoto: Agus Suparto/Indonesia Papal Visit Committee/Anadolu/picture alliance

A cikin kwanaki ukun da jagoran Kiristocin zai yi a Indonisiya, kasar da ke da mabiya addinan Islama miliyan 242, da suka ba ta damar zama kasa mafi yawan Musulmai a duniya, zai gana da shugaban kasa Joko Widodo daga bisa ni kuma ya yi huduba tasalama ga Kiristocin kasar kimanin miliyan takwas.

Dan shekaru 87- da ke fama da rashin lafiya, Paparoma Francis, zai yi kwana 12 yana ziyartar kasashe hudu domin wanzar da alaka mai kyau a tsakanin Kiristoci mabiya darikar Katolika da sauran addinai. Ana sa ran yaziyarci kasashen New Guinea da East Timor da kuma Singapore baya ga Indonisiya da yanzu ya fara da ita. 

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW