1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Paparoma Francis shi ne saban shugaban kiristoci mabiya ɗariƙar Katolika

March 14, 2013

Bayan da suka kwashe kwanaki biyu suna kaɗa ƙuri'a manyan limaman Cocin Roman Katolika sun zaɓi Jorge Mario Bergoglio a matsayin Paparoma.

Newly elected Pope Francis, Cardinal Jorge Mario Bergoglio of Argentina waves from the steps of the Santa Maria Maggiore Basilica in Rome, March 14, 2013. At left is Cardinal Santos Abril of Spain and Cardinal Agostino Vallini, Vicar General of Rome at right. REUTERS/Alessandro Bianchi (ITALY - Tags: RELIGION POLITICS)
Hoto: Reuters

Jorge Bergoglio wanda aka haifa a shekarun 1936 a garin Buenos Aires na ƙasar Argentina a wata shiya da ake kira da sunnan Flores.Ya taso a cikin wasu iyalai masu ɗan abin hannusu, wanda maihaifinsa ɗan asilin ƙasar Italiya ma'aikaci ne a kamfanin sufuri na jiragen ƙasa.

Rayuwarsa ta aiki da karatun da ya yi kafin ya cimma matsayin.

Ya je makarantar gwamnati kamar dukkanin sauran ya'yan talakawa inda a ƙarshe ya kammala karatunsa tare da samin takardar shaida ta ƙorewa a kan aikin kimiyya na Chemistry.

Hoto: picture-alliance/dpa

Yana da 'yan uwa ya'yansa da ƙaunarsa, kuma a lokacin da yi ƙuriciya, ya na sha'awar wasannin ƙwalon ƙafa da ya ke bugawa tare da yaran anguwa waɗanda har yanzu suke tunawa da shi. Bergoglio ya fara samin mu'ijjiza da kuma baiwa, ya na da shekaru 17 a wani Cocin na Saint Jose da ke a cikin shiyar su. Inda manyan mallaman Cocin suka yi la'akari da hazaƙarsa, da kuma ƙaunar da ya ke nuna wa ga talakawa. Ya na da shekaru 22 ya rungumi ɗarikar Jésuite ta 'yan Katolika masu yin dogaro da kuma ba da kai ga Yesu inda ya sami digri na karatun falsafa.

An naɗa shi limamin Cocin a ranar 13 ga watan Disamba na shekara ta 1969, kana a ƙasa da shekaru huɗu ya na da shekaru 36 a duniya aka naɗa shi shugaban yan ɗarikar Jesuit na Argentina. Wanda a yanzu sunnan ne, da ya ɗauka na Francis, na wani tsohon jagoran 'yan ɗarikar mai fafutkar taimaka wa talakawa.

Manufofinsa na yaƙi da auren jinsi ɗaya da kuma zub da ciki.

A lokacin mulkin kama karya na Argentina daga shekarun 1976 zuwa 1983, ya yi ta kokowar ganin an samin haɗin kan yan ɗarikar wanda lamarinsu ya fara samin ɓaraka. kafin a wannan lokaci ya ficce daga Argentina zuwa birnin Fribourg na nan Jamus inda ya yi karatun zama dokta. A cikin watan Mayu na shekara ta 1992 tsohon Paparoma Jean Paul na biyu ya naɗa shi fada na Buenois Aire kafin a shekarun 2001 ya zama Kardinal. Sabon Paparoman yana da ra'ayin yan mazan jiya, kuma yana adawa da lallata, da auren jinsi ɗaya, da kuma zub da ciki. Domin a shekarun 2010 ya yi mumunar adawa ga wata doka a ƙasar Argentina ta aurren jinsi ɗaya.

Hoto: Reuters

Shi ne wani mutumin na farko na yankin Latine Amurika yankin da ke da yawan mabiya ɗarikar Katolika miliyan 500 da aka taɓa naɗawa a matsayin. Kuma jama'a na baiyana shi a matsayin mutumin da ke ƙaunar zaman lafiya.

Daga kasa za a iya sauraron wannan rahoto haɗe da rahotanin da wakilanmu na Najeriya Ibrahima Yakubu daga Kaduna da Mohammed Bello daga yakin Niger Delta su ka aiko mana dangane da ra'ayoyin jama'a a kan zaɓen Paparoma.Daga Nijar kuwa za a iya sauran rahoton da wakilinmu Gazali Abdu Tasawa ya aiko, sai kuma sharhi game da saban Paparoman.

Mawallafi : Abdourahamane Hassan
Edita : Saleh Umar Saleh

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani

Nuna karin labarai