1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rangadin Paparoma don karfafa zaman lafiya a Iraki

Zainab Mohammed Abubakar AMA
March 5, 2021

Mabiya addinin Kirista a Iraki da ke zama tsiraru cikin al'umma na rayuwa  cikin yanayi na tsananci da fuskantar wariya, kuma su na shakkar ko rangadin kwanaki hudu na Paparoma Francis zai kawo wani sauyi.

Irak Besuch des Papst Franziskus
Paparoma Francis a yayin da yake jawabi gaban al'ummar IrakiHoto: Andrew Medichini/AP Photo/picture alliance

Shugaban darikar Roman Katolika Paparoma Francis ya fara ziyarar kwanaki hudu mai taken " dukkanmu 'yan uwan juna ne" a Iraki. Ziyarar da ke zama irinta ta  farko a tarihi a bangaren wani Paparoma a kasar ta Iraki. Shugaban roman katolikan dai zai halarci addu'o'i a majami'un da ke babban birnin kasar, da filin wasan kwallon kafa na birnin Irbil da ke arewaci. Kazalika zai gana da manya limaman musulunci a birnin Najaf da ke kudanci, kafin ya shige zuwa birnin Mosul da jirgi kirar saukar ungulu. 

Shugabannin majami'u dai na bayyana barazanar karewa tsakanin al'ummar musulmi masu rinjayen kasar, inda suka yi hasashen makamancin wannan matsalar a tsakanin kananan al'ummomin kirista kamar yadda lamarin ya kasance da al'ummar Yahudawan Irakin da a baya suke bunkasa. Wasu na cewar a yanzu, kasa da Yahudawa 10 kawai ke zaune a birnin Bagadaza.

Karin Bayani: Fargabar yaki bayan kisan janar din sojan Iran a Bagadaza

An zana hoton PaparomaHoto: AHMAD AL-RUBAYE/AFP via Getty Images

Mabiya addinin kirista dai sun jima da kasancewa a Irakin bisa ga tarihi. Kuma da yawa daga cikinsu basa ganin ziyarar tasa za ta tabuka musu wani abu balle sauya halin da suke ciki. Reemon Youssef Matti da ke zama a sansanin 'yan gudun hijira na Virgin Mary da ke birnin Bagadaza bayan rasa muhallinsa a Ninawa, ya gayyaci Paparoma ya bukaci samar da rigakafin corona ga kowa Paparoma ziyara gani da ido, yana mai cewa " Mu na fatan alkahairi. Amma kada ya je rangadin tituna masu tsabta da ke Bagadaza, ko kuma wurare na musamman da aka tsara saboda ziyarar tasa. Mu na son ya zo nan ya ga yadda abubuwa suke a zahiri. Ya ga yadda rayuwar kiristoci take. Kai mutum ne mai neman zaman lafiya, ka zo ka gane wa idanunka zahiri." Yawancin Kiristocin Irakin dai sun tsere daga biranen arewacin kasar biyo bayan hare-haren mayakan IS a biranen Mosul da Ninawa da kewaye.

Karin Bayani: Damuwa bai kare ba ga yara 'yan kabilar Yazidi a Iraki

Hoton hadin gwiwaHoto: Vatican Media/REUTERS

A shekara ta 1987 dai, kididdigar ya nunar da cewar akwai mabiya addinin kirista miliyan daya da dubu 400. Sai dai cikin shekaru sama da shekaru 30 da suka gabata, mafi yawa daga cikinsu sun kaura. Inda yanzu kididdiga ke nunar da cewar Irakin na da Kiristoci tsakanin dubu 200 zuwa dubu 300 kacal. To sai dai wasu na ganin cewar rayuwar daidaikun kiristocin ba ta cikin hadari kamar yadda yake a baya. Sai dai a ganin Mariam (Wadda kan sakaye cikakken sunanta na gaskiya saboda dalilai na tsaro) kuma mazauniyar birnin Bagadaza, ba a darajawa addinin mutane, tare da cewa "Sama da kwanaki 40 da suka gabata na rasa jikata, don haka muka je neman dan hoton rubutun da zamu rataye a bakin kofar gidanmu. A jikin katakon mun bukaci a rubuta" a cikin sunan Uba da Da da ruhi mai tsarki." Amma shagunan sun ki yarda, domin sabon ubangiji ne. Ban san mun kai wannan matsayi na rashin darajawa addinin wani ba".

Archbishop Warda na Irbil ya na da yakinin cewar, wannan ziyarar ta Paparoma za ta haifar da tambayoyi da tunani mai zurfi. Masu kaifin kishin addini za su yi adawa da ziyara, sai dai mafi yawa daga cikin musulmi za su yi maraba da ita, za su saurareshi, tare da fara binciken ainihin tarihin kiristoci. Wannan shi ne gajiya na dogon lokaci da wannan zira za ta kawo.